Thursday, October 1
Shadow

Kalli Bidiyon: Muna ciyar da Masu laifi Akan Naira 780 kowace rana, hakanan muna ciyar da karnukan aiki akan Naira 800 a kowace rana>>Inji Hukumar gidan gyaran hali ta Najeriya

Hukumar gidan gyaran hali ta Najeriya, Nigerian Prison Service tace tana ciyar da kowane me laifi akan Naira 780 a kowace rana.

Sannan tana ciyar da karnuka akan Naira 800 a kowace rana.

Shugaban hukumar ne ya bayana haka yayin da yake gabatar da kasafin kudin hukumar na shekara a gaban majalisar tarayya.

Sanata Adams Oshiomhole wanda shine ya jagoranci zaman ya kalubalanci cewa, ta yaya za’a rika ciyar da karnuka fiye da mutane?

Karanta Wannan  Mun yi kokarin yiwa Nafiu Bala Gombe Ihisani dan ya hakura karya Kawo mana Tangarda a ADC amma ko kusa ba zamu iya bashi abinda Gwamnati ta bashi ba, dan sun bashi kudi na wuce hankali>>Inji Me Magana da yawun ADC, Bolaji Abdullahi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *