
Tauraron fina-finan Hausa, Musa Mai Sana’a ya bayyana cewa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya masa kyauta ta hannun Ali Nuhu.
Ya bayyana hakane a wani Bidiyo da ya fito yakewa Ali Nuhu da mataimakin shugaban kasar godiya.
Saidai be bayyana irin kyautar da aka masa ba
A baya dai Musa Mai Sana’a ya fito yace ya kashe Miliyoyin Naira wajan yiwa Gwamnatin Tinubu hidima amma ba’a bashi komai ba.
Hakanan Kashim Shettima yawa Adam A. Zango babbar kyauta ta mota.