
Rahotanni nata yawo a kafafen sada zumunta cewa, wai Alpha Charles Borno ta musulunta.
Inda har wani ya fito yake ikirarin cewa wai sune suka musuluntar da ita.
Bidiyon da yayi akan Ikirarin Musuluntar Alpha Charles Borno ya dauki hankula a kafafen sada zumunta inda wasu ke tambayar shin da gaske ta Musulunta?
Alpha Charles Borno takan yi abubuwa masu daukar hankali dake nuna irin soyayyar da takewa musulmai da kuma yabon Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) a wasu Lokutan.
Saidai binciken da hutudole ya gudanar, bai tabbatar da musuluntar Alpha Charles Borno ba.
Bayan duba shafukanta na sada zumunta, Babu inda Alpha Charles Borno tace ta musulunta, kuma lura da hakan abune me muhimmanci a rayuwa, da matukar wuya ace ta musulunta bata sanar da hakan a shafinta na sada zumunta ba.