
‘Yar Siyasa daga yankin Arewa, Naja’atu Muhammad ta yi zargin cewa Donald Trump na America ne ke mulkin Najeriya ba shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ba.
Ta bayyana hakane a wata hira da DCL Hausa ta yi da ita.
Tace tunda Najeriya ta samu ‘yancin kanta Najeriya bata taba yadda sojojin wata kasa sun shigo cikinta sun kawo hari ba sai lokacin Tinubu.
Tace a yanzu Turawa na kara yi mana Mulkin mallaka ne da aka yi a shekarun baya.