Thursday, January 8
Shadow

Kalli Bidiyon: Tsohon Shugaban Buhari ya yi ta neman Masu gaskiya irinsa da zai baiwa Mukami amma ya kasa samun ko da mutum daya>>Inji Hadimin Shugaban kasar, Malam Bashir Ahmad

Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya nemi wadanda zai baiwa mukaman Siyasa masu gaskiya da kishin Najeriya irinsa amma ya kasa samu.

Hadiminsa, Malam Bashir Ahmad ne ya bayyana hakan a wata hira da Ali Jita yayi dashi.

Yace Buhari ya gaya musu cewa a tsawon lokacin da ya dauka yana kokarin neman Mulki, ya manta bai nemi mutane nagartattu ba da zai yi aiki dasu.

Yace sai bayan da ya ci zabe, ya je gida ya kwanta amma Bacci ya ki zuwa, yace sai ya tuna wata ma’aikata da ke da matsala, sai yayi tunanin wanene zai dakko me irin ra’ayinsa ya baiwa wannan ma’aikata amma sai ya kasa samun ko da mutum daya.

Karanta Wannan  Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un: Kalli Bidiyon yanda aka kama wata Yarinya da aka tura Islamiya a Otal

Yace a wannan lokacinne yasan cewa bai samarwa kansa abokan aiki ba.

@realalijita

“Kalubalen Nijeriya, gwamnati, da gaskiyar da ba kowa ya sani ba — Bashir Ahmad.” Acikin shirin zauren jita na satin nan @ YouTube Ali jita multimedia channel

♬ original sound – Ali Jita

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *