
A ‘yan kwanakinan kamen ‘yan Arewa Hausawa da fulani na karuwa a jihohin Yarbaw da Inyamurai.
Ana kama wadanda yawanci ‘yan ciranine ana makala musu sunan garkuwa da mutane.
Saidai da yawan ‘yan kudun dake shahi akan wadanda ake kamawan na bayyana cewa ya kamata a tsananta bincike dan wadanda ake kamawa din basa kama da masu garkuwa da mutane.
Lamarin dai ya jawo zazzafar muhawara a kafafen sadarwa.