Wednesday, January 15
Shadow

Kalli Bidiyon yanda aka hada irin dakin Ka’aba a Najeriya dan koyawa Alhazai yanda zasu yi aikin Hajji, saidai wasu sun ce hakan Bidi’a ne saboda Annabi(SAW) bai ce a yi ba

Bidiyon yanda aka hada irin dakin Ka’aba a Najeriya ake koyawa mahajjata yanda zasu yi aikin Hajji ya watsu a shafukan sada zumunta.

Mutane da yawa sun bayyana mabanbanta ra’ayoyi akai.

https://twitter.com/LifeSaudiArabia/status/1795470560224583895?t=CHtszFt-1PKa3DNX791TJw&s=19

Akwai wanda suke ganin cewa babu abinda Ma’aiki, Annabi Muhammad(SAW) ya bari be koyar da al’umma ba dan haka yin wannan abu tunda annabi(SAW) bai yi ba kuma bai ce ayi ba bai kamata ba.

A bidiyon dai an ga wani daki me kama da na ka’aba, mutane sanye da fafaren kaya suna zagayashi, kamar dai a Makkah.

Saidai inda mutum zai gane ba dakin ka’aba bane, ga mutane na gefe suna kallo, sannan kuma ga gurin kasa ne, ba kamar a saudiyya ba.

Karanta Wannan  ALLAHU AKBAR: Ya Rasu A Yau Asabar Bayan An Yi Gama Hawan Arfa Da Shi A Makkah

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *