
Shahararren mawakin Batsa na Arewacin Najeriya, SojaBoy ya bayyana damuwa bayan da jirgin saman da ya hau daga Legas zuwa Abuja yaki Tashi.
Ya wallafa Bidiyon faruwar lamarin a shafinsa na sada zumunta inda yace da kyar aka bari suka fito daga cikin jirgin yayin da zafi ya damesu.
Lamarin dai ya dauki hankula inda wasu ke cewa rashin bin doka ne yasa hakan daga bangaren masu safara da jiragen.