
Wani sojan Najeriya yayi bayanin Albasinda akw biyansu dalla-dalla tun daga fara aiki har ka gama.
Saidai yayi maganane akan kurtu inda yace yayi wannan bayanine musamman ga wadanda ke son shiga aikin na soja.
Yace albashin farko idan aka daukeka aiki Naira 104,000 ne.
Daga nan ne idan ka shekara 5 aka kara maka matsayi, zaka samu karin Albashin zuwa Naira 112,000.
Yace idan mutum yayi shekaru 10 za’a kara masa albashi zuwa Naira 115,000.
Yace idan ka shekara 15 za’a kara maka albashi zuwa Naira 125,000.
Yace idan ka shekara 20, za’a kara maka albashi zuwa Naira 150,000.
Yace amma akwai alawus na Naira dubu 20 duk wata da ake biyansu.