Saturday, December 6
Shadow

Kalli Bidiyon yanda Sojojin Sama suka yi amfani da lema suka fice daga cikin jirgin yàkìn su da ya kama da wùtà a jihar Naija

Jirgin sama na rundunar sojojin sama ta Najeriya yayi hadari a jihar Naija.

Jirgin ya tashi ne a sansanin sojin dake Kainji inda jim kadan da tashinsa ya samu matsala.

Jirgin na daukene da sojojin sama biyu amma sun samu damar ficewa daga ciki kamin ya fadi.

shugaban sojin saman Najeriya, Air Marshal Sunday Kelvin Aneke ya jinjinawa kokarin da sojojin suka yi na karkatar da jirgin bai fada kan mutane ba.

Yace sojojin na cikin koshin lafiya kuma ana kara duba lafiyarsu.

Karanta Wannan  Shugaba Tinubu ya haramta sayo kayan da ake iyayi a cikin gida daga kasashen waje

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *