Bidiyon yanda wani balarabe ke dukan bakar fata ya watsu sosai a kafafen sada zumunta inda abin ya jawo Allah wadai.
An ga yanda aka daure bakar fatar a kan kujera ana dukansa da sanda.
Babu dai cikakken bayani kan dalilin faruwar hakan.
Mutane da yawa daga kasashen Africa ne ke zuwa kasashe irin na larabawa da turawa dan neman abin yi.