Wannan Zainab ce wadda kusan duk masu bibiyar kafafen sada zumunta sun santa.
Diyace a wajen marigayi, sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero wadda rayuwarta ke cikin damuwa da rashin tabbas.
A sabon bidiyon da ta yi ta bayyana cewa gata karfe dayan dare a Birnin Legas tare da mahaifiyarta da kaninta wanda kuma akanta suka dogara.
Tace mahaifinta ya barta ba ilimi ba wani abu da zata iya dogaro dashi, bata da aikin yi.
Tace ta gaji bata san yadda zata yi ba, babu wanda ke taimakonta.
A baya dai Gwamnatocin Ganduje dana Abba Gida-Gida sun taimaka mata.
A wannan karin, Hadimin tsohon shugaban kasa, Malam Bashir Ahmad yayi kiran da a sake taimakawa Zainab, musamman Gwamnatin jihar Kano.