
Babban Malamin coci, Rev. Ezekiel Dachomo ya bayyana cewa zai kai Najeriya kotun Duniya.
Yace ya riga ya kaita kotun Allah kuma kwanannan mala’iku zasu sakko su yi maganin masu muzgunawa Kiristoci.
Ya bayyana hakane yayin ganawa da manema labarai inda yace kuma sun jinjinawa Shugaban Amurka, Donald Trump saboda zuwan da yayi Najeriya.