Sunday, January 11
Shadow

Kalli Hoto: Nuna wayar ta ta iPhone 17 Pro Max ta jawowa kakakin ‘yansandan jihar Akwa-Ibom cece-kuce inda da yawa ke cewa Albashinta bai isa ya saya mata wayar ba

Kakakin ‘yansandan jihar Akwa-Ibom, Timfon John ta dauki hankula bayan da aka ganta rike da wayar iPhone 17 Pro max ta Naira Miliyan 2.5 a yayin da Albashinta bai wuce Naira 300,000 ba.

Da yawa dai sun rika caccakar ta da cewa ina ta samo wayar dan Albashinta dai ba zai iya saya mata wayarba.

Saidai kakin ‘yansandan jihar Delta, Bright Edafe ya kare abokiyar aikin nasa inda yace watakila ta tara kudinne ta siya.

Yace akwai wanda da gaske suna satar amma an zuba musu ido.

Karanta Wannan  Gwamnatin Amurka zata fara bukatar 'yan Najeriya dake son zuwa kasar su ajiye dala $15,000(Naira Miliyan Asihirin da biyu) idan mutum ya dawo gida za'a mayar masa da kudinsa, idan kuma ya ki dawowa za'a rike kudin

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *