Wednesday, January 15
Shadow

Kalli Hoton matar da kotu ta yankewa hukuncin kis-sa ta hanyar ra-ta-ya a jihar Kebbi saboda kash-she mijinta, saidai tace bata yadda a kash-sheta ba, zata daukaka kara

Babbar Kotu a jihar Kebbi ta yankewa Fatima Abubakar hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samunta da laifin kashe mijinta Attahiru Muhammad-Ibrahim.

Lamarin ya farune a ranar 25 ga watan Augusta na shekarar 2022 inda Fatima ta cakawa mijin nata wuka a ciki.

Mai shari’a, Justice Umar Abubakar ne ya yanke wannan hukunci inda yace sun samu hujjoji masu karfi dake nuna cewa lallai Fatima ce ta kashe mijinta.

Yace kuma an yanke mata hukuncin daurin shekaru 7 a gidan yari saboda azabtar da mijin nata da ta yi.

Saidai lauyan Fatima, Sani yace zasu daukaka kara.

Karanta Wannan  Me ake nufi da aure

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *