Friday, January 23
Shadow

Kalli Hotuna: Barayi sun yi yunkurin yin sata a yayin da Gobarar Amurka ke ci

An kama wasu barayi da suka yi yunkurin yin sata a yayin da gobarar garin Los Angeles na jihar California kasar Amurka ke ci.

A yayin da ake neman masu kashe gobara saboda karanci kuma mutane da yawa ke guduwa suna barin gidaje da dukiyoyinsu, wadannan bata gari su kuma sata ce suka sa a gaba.

Zuwa yanzu mutane 4 ne mahukuntan jihar suka fitar da hotunansu a matsayin barayin.

Gobarar dai ta kone gidaje sama dubu goma sha biyu inda masu kashe gobara sama da dubu goma sha hudu ke ta kokarin kasheta.

Karanta Wannan  Jigo a Jam'iyyar PDP, Segun Sowunmi yace a shirye yake ya koma APC duk da a baya ya soki jam'iyyar

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *