
Sojojin Najaria sun kafa tutar Najeriya bayan kwace iko da wata maboyar ‘yan Bindiga a jihar Zamfara.
Sojojin dai sun dage da matsawa ‘yan Bindiga inda suka kashe da dama wasu kuma suka tuba suka mika makaman hannunsu.
Nasara ta kwanannan da sojojin suka samu itace wadda suka kai Ruwan Kunku inda suka kone gidajen ‘yan Bindigar.