
Attajirin dan kasuwa, Aliko Dangote ya sha Alwashin karya farashin Shinkafa inda yace zai kafa kamfanin shinkafar a jihar Naija.
Hakan na zuwane kwanaki bayan da BUA ya sha Alwashin karya farashin shinkafar.
Babbar me baiwa shugaban kamfanin na Dangote shawara Fatima Abdurrahman ce ta bayyana haka inda tace aina gina kamfanin shinkafar ne a Wushishi.
Tace shirin gina kamfanin yana karkashin hadaka ne da Gwamnatin jihar Naija ke yi da kamfanoni masu zaman kansu.