Kamfanin BUA ya yi karin haske kan rahotanni dake yawo suna cewa ya kusa kammala matatar man fetur da yake ginawa a jihar Akwa-Ibom.
Rahotanni sun bayyana cewa, aikin gina matatar ya kai kaso 90 cikin 100.
Saidai a sanarwar da kamfanin ya fitar, yace wannan ikirarin ba gaskiya bane, tabbas yana kan aikinsa na gina mamatar man fetur din wadda zara rika samar da ganga 200,000 duk kullun amma maganar an kai kaso 90 cikin 100 na ginata ba gaskiya bane.
Kamfanin ya kara da cewa, bayan Mamatar man fetur din akwai kuma tashoshin gas na CNG da zai gina.