Thursday, January 2
Shadow

Kamfanonin sadarwa sun yi barazanar mayar da sabis karɓa-karɓa

Ƙungiyar masu kamfanonin sadarwa a Najeriya ta yi gargadin cewa za a iya fuskantar katsewar network matuƙar ba a sauya tsarin yadda suke cajar kuɗaɗe a fannin sadarwa ba duk da yadda suke gudanar da ayyukansu ke ƙara tsada.

Shugaban ƙungiyar masu kamfanonin sadarwa da ke da lasisi a Najeriya Gbenga Adebayo ne ya bayyana hakan a yau Litinin cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce ɓangaren sadarwa na tsaka maki wuya saboda tashin gauron zabi da ake fuskanta sakamakon tashin farashin kayayyaki, da rashin tabbas a kasuwar musayar kudi da kuma tashin farashin makamashi.

Cikin sanarwar Mista Adebayo yace duk da ƙalubalen da ake fuskanta na gudanarwa, har yanzu ba su ƙara kuɗaɗen da suke cajar mutane ba, wani abu da yake barin masu kamfanonin cikin mawuyacin hali wajen kiyaye ingancin aikin da suke gudanarwa.

Karanta Wannan  Ji yanda Magidanci ya zubawa matarsa man fetur ya bankawa mata wuta

Shugaban ƙungiyar ya ce matuƙar ba a dauki mataki kan kudaden da suke cajar mutane ba a ƙara su, to za a iya fuskantar taƙaitar sabis a wasu yankuna.

Ya ce yayin da ake shirin shiga sabuwar shekara masu kamfanoni na shirin taƙaita bayar da sabis a wasu yankuna duk kuwa da cewa sun san hakan zai iya haifar da koma bayan tattalin arziƙi da katsewar kasuwancin da suka dogara kacokan kan intanet.

A 2025, wuraren gwamnati irinsu Bangaren tsaro da ilimi da lafiya da kuma kasuwanci da suka dogara kan kamfanonin sadarwa wajen aikinsu za su fuskanci katsewar network.

Za a mayar da sabis tamkar yadda ake yi wa wutar lantarki a bayar a wannan yankin a ɗauke a wannan yankin, matuƙar ba a yi wa tufkar hanci ba.

Karanta Wannan  Kalli Kayatattun hotunan Rahama Sadau

Ya ce nauyin da ke wuyar kamfanonin sadarwa na neman durƙusar da su, don haka an kai matuƙar da ba za su iya ɗauka ba, wanda hakan ya sa ba za su iya gudanar da aikinsu ba a zamanance saboda tsadar lamura.

A watan Afrilun wannan shekarar ne kamfanonin suka fara kuka kan a ba su damar ƙara kudaden da suke caji, amma har ya zuwa yanzu ba a samu wani ci gaba ba.

A wani mataki na nuna damuwa kan matsalar tattalin arziki da fannin yake fuskanta, ALTON ta nemi gwamnatin tarayya ta yi zaman tattaunawa da masu ruwa da tsaki a harkokin sadarwa.

Kungiyar ta ce akwai buƙatar fitar da wani tsari da zai daidaita yadda za su riƙa caji da kuma yadda abokan hulɗarsu za su iya biyan abin da za a caje su domin fanni ya ci gaba da ɗorewa. Bayan shekaru 11 da aka yi da tsarin cajin kuɗi guda.

Karanta Wannan  Gwamnan Jihar Katsina, Malam Umar Dikko Radda, Ya ƙaddamar da motocin sufuri a Jihar Katsina

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *