Friday, January 24
Shadow

Kan mu ya daure, Bamu san wanne hukunci zamu yi amfani dashi ba>>Hukumar ‘yansandan jihar Kano bayan da aka aika mata hukunce-hukuncen kotu har 5 da suka shafi masarautar Kano, saidai ta bayyana abinda zata yi nan gaba

Hukumar ‘yansandan jihar Kano ta bayyana tsaka mai wuya da take ciki kan hukunce-hukuncen kotu har guda biyar da aka yi kan masarautar Kano.

Kwamishinan ‘yansandan jihar, Mr Usaini Gumel ne ya bayyanawa manema labarai hakan inda yace sun tattara duka wadannan hukunce-hukuncen 5 sun aikewa da shugaban ‘yansanda na kasa yayin da shi kuma ya aikawa da ministan shari’a.

Yace suna jiran ministan shari’ar ya gaya musu da wane hukunci zasu yi amfani.

Yace da zarar sun samu umarni daga ministan shari’ar, zasu zartas da hukuncin da doka ta amince dashi.

Yayi kira kan kafafen yada labarai da su rika tantance labari kamin su yadashi.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo yanda NLC ta kulle gidan rarraba lantarki na Kaduna(KEDCO)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *