Wednesday, January 15
Shadow

Kanfanonin dake hako danyen man fetur a Najeriya sun ki sayar min dashi, sun kwammace su kaishi kasashen waje>>Dangote

Babban Attajirin Afrika, Aliko Dangote ya bayyana cewa, kamfanonin dake hako man fetur a Najeriya basa son sayar masa da danyen man fetur din.

Ya bayyana hakane a hirar da gidan talabijin na CNN suka yi dashi inda yace kamfanonin sun saba da kai man fetur kasashen waje suna samun kudi dan haka sun ki sayar masa da danyen man.

Yace da za’a sayar masa da danyen man, babu bukatar a rika sayo tataccen man daga kasashen turawa.

Yace amma ‘yan kasuwa dake shigo da man fetur din daga kasashen waje basa son hakan dan kuwa zasu rasa aiki.

Saidai gwamnatin Najeriya ta bakin hukumar dake kula da harkar man fetur din, NUPRC, ta bayyana cewa zasu shiga tsakanin Dangote da kamfanonin dake hako man fetur din.

Karanta Wannan  Hotuna: Dangote ya kaddamar da kamfanin hada manyan motoci a Legas

Wakilin hukumar, Olaide Shonola ne ya bayyana haka a hirar da jaridar Punch ta yi dashi inda yace dama can suna shiga tsakanin Dangoten da kamfanonin amma zasu kara kaimi.

Yace ba zasu iya tursasa kamfanonin ba amma zasu yi abinda doka ta basu damar yi na baiwa kamfanonin umarnin sayarwa da Dangoten danyen man.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *