
Gwamnatin jihar Edo ta musanta ikirarin kungiyar IPOB dake cewa ta biya Biliyan 6 a matsayin diyyar mafarauta 16 da aka kashe aka Kona a jihar.
Kakakin Gwamnatin jihar, Fred Itua yace maganar kungiyar IPOB ba ba gaskiya bace, basu bayar da naira Biliyan 6 a matsayin kudin diyyar kisan wadannan mafarauta da aka kona ba.
Yace maganar ta IPOB kawai sun yi tane dan kawo hargitsi da gwara kawunan mutane.
Dan haka ya bukaci mutane su yi watsi da wannan magana.