Friday, December 5
Shadow

Karya ake mana, Bamu ce Muna goyon bayan Tinubu a zaben shekarar 2027 ba>>Tsaffin ‘Yan Majalisar tarayya

Tsaffin ‘yan majalisar tarayya sun bayyana cewa, ba gaskiya bane kudin goro da aka musu aka ce wai suna goyon bayan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a zaben shekarar 2027.

Tsaffin ‘yan majalisar sun yi taronsu a Abuja wanda shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila ya shirya inda ya roki takwarorinsa daga Arewa su marawa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu baya a zaben shekarar 2027.

Yace ko dan shugaban kasar ya kammala ayyukan ci gaba da ya faro a Arewa, ya kamata su mara masa baya.

Bayan taron an fitar da sanarwa dake cewa, tsaffin ‘yan majalisar sun amince su marawa shugaba Tinubu baya.

Karanta Wannan  Karuwanci ya kaita jihar Legas>>Hadimin Shugaban kasa ya zargi matashiya 'yar Bautar kasa data soki Shugaba Tinubu

Saidai wasu daga cikin tsaffin ‘yan majalisar bisa jagorancin Rufa’i Chanchangi sun bayyana cewa ba gaskiya bane wannan ikirari.

‘Yan majalisar da suka ce basu tare da Tinubu sune, Hon. Zakari Mohammed; Hon. Aminu Shagari; Hon. Tom Zakari; Hon. Mohammed Musa Soba; da Hon. Chika Adamu.

Sun ce Akwai karuwar Talauci a Arewa, matsalar tsaro, da rashin aikin yi tsakanin matasa, da tafiyar matasa zuwa Cirani a karkashin mulkin Tinubu.

Sun ce maganar gaskiya akwai damuwa sosai da talauci a Arewacin Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *