Saturday, July 25
Shadow

Karya Tsohon shugaban DSS, Dennis Amachree yawa tsohon shugaban kasa, Janar Sani Abacha, Bai rasu ba yana Laalata da Budurwarsa ba>>Inji Tony Eluemunor

Dan jarida dake aiki da Vanguard, Tony Eluemunor ya karyata tsohon shugaban DSS, Dennis Amachree da yayi ikirarin cewa wai tsohon shugaban kasa, Janar Sani Abacha ya rasu ne yana tsaka da Laalata da Budurwarsa.

Tony yace labarin da Amachree ya bayar ba abun kamawa bane, yace ta yaya kawai mace zata gaya maka magana kawai babu wata hujja babu wani bincike kace ka yadda?

Tony yace abinda Amachree ya fada fahimtarsa ce sannan yace bayan ya kammala yiwa budurwar Abacha da ake zargi Tambayoyi ya aikata Abuja, yace amma bai gaya mana yanda hukumar DSS ta kammala binciken matar ba.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Yanda Sowore ya je hedikwatar 'yansanda dan ya ga sabon IGP, Disu da shugaba Tinubu ya nasa, saidai 'yansanda da yawa sun ce mas su basu ma san an nada sabon IGP ba

Yace maganar gaskiya a daren da Abacha zai rigamu gidan gaskiya, akwai wasu mata ‘yan kasar Philippines 2 da suka je ya gana dasu.

Yace kuma ko su ba wai Abacha yayi lalata dasu bane, saboda a wannan dare yana cikin matsananciyar rashin lafiya.

Yace bayan Abacha ya kammala ganawa da wadancan matan ne yana kan hanyar komawa gida ya yanke jiki ya fadi akan matakalar bene.

Yace Abacha na fama da cutar Numfashi ta Asama amma a ranar bai dauki inhala da maganinsa zuwa ganawa da wadannan matan ba saboda yasan ba dadewa zai yi, a lokacin da cutar ta tasar masa, ihlarsa bata kusa dashi.

Karanta Wannan  A karshe dai Sojoji sun kubutar da matar Marigayi Janar Rabe

Yace kuma aiki na karshe da Abacha yayi a hukumance shine raka tsohon shugaban Falas2,Yasser Arafat filin jirgi bayan ziyarar da ya kawo masa.

Yace a cikin jami’an tsaron da Yasser Arafat ya zo dasu ne ake zargin daya ya watsawa Abacha guna ta hanyar biro wanda an ga hakan a Bidiyon da aka dauka yayin ziyarar.

Yace Yasser Arafat na barin Najeriya, Rashin lafiyar Abacha ta tsananta sosai.

Yace dama kuma a lokacin kasashen yamma na ta fakon yanda zasu kawar da Abacha saboda ya zamar musu karfen kafa.

Yace dan haka Amachree karya yake.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *