Kasar Jamus dake Nahiyar Turai ta bude damar daukar ‘yan Najeriya da sauran kasashen Duniya aiki inda take neman mutane akalla 400,000.
Ana daukar aikinne na mutane masu basira ta kafar yanar gizo.
Ofishin kula da harkokin kasashen waje na kasar Jamus din ne ya fitar da wannan sanarwar a ranar 1 ga watan Janairu.
Wadanda ke son yin aiki a kasar ta Jamus ko haduwa da iyalansu dake can ko yin karatu duka na iya neman zuwa kasar.
Ministar Harkokin waje ta kasar Jamus din, Annalena Baerbock ta bayyana cewa, ta wannan hanyar, zasu samu kwararrun ma’aikata da zasu taimakawa karfafa tattalin arzikinsu.