Kasa da mako daya bayan da kasar Nijar ta dawo da ‘yan Najeriya su 310 zuwa gida Najeriya, kasar ta sake taso keyar wasu karin mutane 392 zuwa Najeriya.
Hakan ya kawo jimullar ‘yan Najeriya da aka dawo dasu gida daga kasar Nijar zuwa 702 a cikin sati daya.
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa, NEMA da sauran hukumomi masu ruwa da tsaki a lamarinne suka tarbi ‘yan Najeriyar da aka koro daga Nijar a Titin Airport Road dake Kano.
Hukumar ta NEMA ta tabbatar da hakan a wata sanarwa da ta fitar ta shafinta na X.