Thursday, December 26
Shadow

Kasar Pakistan ta kaiwa Afghanistan hari inda mutane 46 suka mutu

Rahotanni daga kasar Pakistan na cewa, kasar Afghanistan ta kai mata hari da jiragen yaki na sama wanda suka yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 46.

Wadanda suka mutun wanda yawanci matane da kananan yara kamar yanda gwamnatin kasar ta Afghanistan ta tabbatar.

Hakanan akwai karin mutane 6 da suka mutu sanadiyyar karin wasu hare-haren da kasar ta Pakistan ta kai a kasar ta Afghanistan.

Ma’aikatar harkokin kasashen waje ta Afghanistan tuni ta kira wakilin jakadan Pakistan dake kasarta inda ta yi Allah wadai da lamarin tare da shan Alwashin kai harin ramuwar gayya.

Kafar Reuters tace kasar Pakistan ta kaiwa ‘yan Bindigar TTP harine biyo bayan harin da suka kai a kudancin Waziristan daya kashe sojojin Pakistan din guda 16.

Karanta Wannan  Gwamnati ta sake kara farashin man fetur zuwa Naira 1070 akan kowace lita

TTP ta hada kai da Kungiyar Taliban amma tana kai harine bisa radin kanta ba tare da katsalandan daga Talibàn.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *