Wednesday, May 7
Shadow

Kashim Shettima yayi magana bayan rahoton cewa an hanashi shiga fadar shugaban kasa ya yadu

Ba wanda ya hana ni shiga fadar shugaban kasa – Kashim Shettima

Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya bayyana rahotannin da ke yawo cewa an hana shi shiga fadar shugaban kasa a matsayin karya maras tushe.

Daily Trust ta rawaito cewa a daren jiya Juma’a ne wasu rahotanni su ka fito daga wata kafar labarai ta yanar gizo suna cewa an hana Mataimakin Shugaban Kasa shiga fadar shugaban kasa ta hannun wasu jami’an tsaro, tare da cewa an killace shi a gidansa har sai shugaban kasa ya dawo daga tafiyarsa ta kasashen waje.

Amma cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Asabar, Mista Stanley Nkwocha, mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai a ofishin mataimakin shugaban kasa, ya ce: “A ‘yan kwanakin nan, an shirya kuma an tsara yada labaran karya da gangan akan Mataimakin Shugaban Kasa da ofishinsa ta hanyoyi daban-daban.

Karanta Wannan  'Yan Najeriya 203 da suka maƙale a Libya sun koma gida

“Wadannan rahotannin na karya da aka shirya da mugunta suna da nufin jefa rudani da kuma kirkirar rikici a tsakanin manyan masu mulki a kasar. Ana kokarin yaudarar jama’a ne domin su yi tunanin cewa akwai sabani a matakin kololuwa na gwamnati.”

Nkwocha ya ce: “Na baya-bayan nan daga cikin jerin wadannan labaran karya shine rahoton da ke cewa an hana Mataimakin Shugaban Kasa shiga Fadar Shugaban Kasa. Wannan yunkuri ne mara karfi na bata suna da ofishin Kashim Shettima. Don tabbatarwa, BA WANI ABU MAKAMANCIN HAKA DA YA FARU.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *