Firaiministan Israel, Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa ko da an yi sulhu tsakaninsu da kungiyar Hamas wa’adin sulhun na karewa zasu ci gaba da yaki a Gaza.
Yace suna fatan a yin sulhun amma ba zasu daina yaki ba har sai sun cimma muradinsu na yin yakin a Gaza.
Masu shiga tsakani dai sun bayyana damuwa akan matsayin da Firaiministan Israel ya dauka.
Israel na son cimma kawar da kungiyar Hamas a matsayin kungiya me rike da makamai ko kuma kungiyar siyasa, kwato duka wadanda aka yi garkuwa dasu da kuma hana Gaza zama barazana ga Israel nan gaba.
Kungiyar Hamas dai ta ki amincewa ta saki mutanen da take gasrkuwa dasu su 100 inda itama ta gindaya sharudanta.