Monday, December 16
Shadow

Ko NLC na iya tilasta wa gwamnoni biyan albashi mafi ƙanƙanta?

Ƙungiyar ƙwadago NLC, ta Najeriya ta umarci ma’aikata a jihohin da gwamnatocinsu ba su aiwatar da sabon tsarin albashi mafi ƙanƙanta ba da su shiryawa tsunduma yajin aiki nan da ranar 1 ga watan Disamba.

Ƙungiyar ƙwadagon ta bayyana cewa jan ƙafar da jahohin ke ci gaba da yi wajen aiwatar da sabon tsarin albashin, wani nau’in cin zarafi da tauye hakki ne.

Kungiyar kwadagon ta bayyana umurnin a cikin wata takardar bayan taro da shugabanta, Mista Joe Ajaero ya fitar, lokacin da suka kammala taron majalisar zartarwa ta ƙungiyar a birnin Fatakwal.

NLC ta nuna da damuwa da rashin amincewa da jan kafar da wasu jihohin a Najeriya ke ci gaba da yi wajen aiwatar da tsarin albashin mafi karanci na 2024, kuma a cewar ta abu ne da ya saba ma doka, tare da taushe hakkin ma’akata musammam a wannan yanayi na matsin rayuwa.

Karanta Wannan  Babu Wata Doka A Nijeriya Da Ta Haramta Tuhumar Kananan Yara Idan Sun Yi Laifi, Tausayin Ne Kawai Ya Sa Tinubu Ya Yafewa Yara Masu Źanga-Źanga, Inji AGF

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *