
Gwamnatin tarayya ta gargadi ‘yan siyasa masu tururuwar komawa jam’iyyar APC da cewa komawa jam’iyyar ba zai sa a dakatar da binciken da ake musu ba.
Babban lauyan gwamnati, Prince Lateef Fagbemi, SAN ne ya bayyana haka ta bakin kakakinsa, Mr. Kamarudeen Ogundele inda yace Gwamnatin tarayya zata ci gaba da tabbatar da doka da oda.
Yayi maganar ne bayan da me magana da yawun Atiku Abubakar yayi zargin cewa wasu manyan gwamnati sun gana da wani gwamnan jihar Kudu maso Kudu kamin ya koma APC.
Fagbemi yace babu gaskiya a wannan ikirari inda yace yana kiran a yi watsi da maganar.