Monday, August 10
Shadow

Komowa jam’iyyar APC ba zai sa a dakatar da binciken da ake maka ba>>Gwamnatin Tarayya ta gayawa ‘yan siyasa

Gwamnatin tarayya ta gargadi ‘yan siyasa masu tururuwar komawa jam’iyyar APC da cewa komawa jam’iyyar ba zai sa a dakatar da binciken da ake musu ba.

Babban lauyan gwamnati, Prince Lateef Fagbemi, SAN ne ya bayyana haka ta bakin kakakinsa, Mr. Kamarudeen Ogundele inda yace Gwamnatin tarayya zata ci gaba da tabbatar da doka da oda.

Yayi maganar ne bayan da me magana da yawun Atiku Abubakar yayi zargin cewa wasu manyan gwamnati sun gana da wani gwamnan jihar Kudu maso Kudu kamin ya koma APC.

Fagbemi yace babu gaskiya a wannan ikirari inda yace yana kiran a yi watsi da maganar.

Karanta Wannan  Wani Malamin Addinin Islama daga kasar Yarbawa ya dauki hankula bayan da yace wai idan ka gayawa Saniya cewa Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) ya yi Wafati zaka ga Bàlà'i, ba zaka koma gida Lafiya ba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *