Saturday, June 27
Shadow

Kotu Ta daure Tsohon Akanta janar na Najeriya Chukwunyere Anamekwe Nwabuoku tsawon shekaru 72 saboda satar Naira Miliyan N868.4

Babbar kotun tarayya dake Abuja ta daure tsohon Akanta Janar na kasa, Chukwunyere Anamekwe Nwabuoku bayan samunsa da laifin satar kudade da suka kai Naira Miliyan N868.4

Mai shari’a, Justice James Omotosho ne ya yanke masa hukuncin ranar Litinin bayan gamsuwa da hujjojin da aka gabatar masa kan zargin.

An zargeshi da saka kudi a wasu asusun bankunan kamfanoni 4 wanda a baya ya karyata yace bai ma taba jin sunayen kamfanonin ba.

Saidai daga baya ya amsa cewa lallai ya tura kudade zuwa asusun ajiyar kudi na wadannan kamfanonin.

Kamfanonin sune kamar haka: Temeeo Synergy Concept Limited, Turge Global Investment Limited, Laptev Bridge, sai kuma Arafura Transnational Afro Limited.

Karanta Wannan  DA DUMIDUMINSA: Gwamna Bala Na jihar Bauchi Ya Bada Umurnin A Mayarwa Da Almajiran Marigayi Sheikh Idris Dutsen Tanshi Filin Idi Na Games Village Da Aka Kwace A Baya

Chukwunyere Anamekwe Nwabuoku a yanzu dai shekarunsa 64 a Duniya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *