Thursday, August 13
Shadow

Da Duminsa: DSS sun sake kai samame gidan Tsohon Ministan shari’a Abubakar Malami

Rahotanni sun bayyana cewa, DSS sun sake kai samame gidan tsohon Ministan shari’a Abubakar Malami a yau, Litinin.

Samamen na DSS na zuwa jim kadan bayan da tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya kaiwa Abubakar Malami ziyara gidan nasa.

Rahotanni wanda Sahara Reporters ta ruwaito, tace DSS sun zagaye gidan na Malami yayin da Atiku ya kai masa ziyara, kuma bayan da Atikun ya tafi ne sai suka afka cikin gidan suka kori kowa daga ciki.

Hakan na zuwane dai yayin da ake zargin gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da yunkurin murkushe ‘yan Adawa kamin zaben shekarar 2027.

Karanta Wannan  Wasu Mahalarta Taron Mauludin Kano Kenan Cikin Shauki Yayin Da Suka Ce Sun Ga Shehu Inyass A Cikin Fitilar Filin Taron

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *