Friday, December 5
Shadow

Kotu ta hana tsohon Gwamnan jihar Kogi, Yahya Bello Fasfo dinsa inda yace yana son ya je kasar waje a duba lafiyarsa, Saidai kotun tace bai bayar da hujjar cewa Likitocin Najeriya ba zasu iya magance rashin lafiyar tashi ba

Babbar Kotun tarayya dake Maitama Abuja ta hana tsohon gwamnan jihar Kogi Yahya Bello Fasfo dinsa dan ya je kasar waje neman magani.

Mai shari’a Justice Emeka Nwite ya bayyana wannan hukunci.

Yace takardun da Tsohon gwamnan ya gabatar na neman ya tafi kasar ingila basu da tambarin sarki wanda kotun tace basu da wani amfani a wajanta.

Dan haka tace kuma rashin lafiyar ta tsohon gwamnan ba ta yi tsananin da za’a ce sai an fitar dashi kasar waje ba.

Ana zargin tsohon gwamnan da dan uwansa, Ali Bello, Dauda Suleiman da Abdulsalam Hudu wajan satar Naira N80, 246,470, 088.88.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Ba kowane hadisi ake yadda dashi ba>>Sheikh Dr. Ahmad Gumi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *