Kotun daukaka kara ta Kano a yau Juma’a, ta yi watsi da umarnin babbar kotun da ta soke nadin Sanusi Lamido Sanusi a matsayin Sarkin Kano na 16.
Wani kwamitin mutane uku na kotun daukaka kara, a hukuncin da ta yanke, karkashin jagorancin mai shari’a Mohammed Mustapha, ya yi watsi da hukuncin da kotun tarayya ta yanke a ranar 20 ga watan Yuni, 2024, ƙarƙashin mai shari’a Abubakar Liman, na babbar kotun tarayya, wanda ya soke dokar masarautar Kano ta 2024 da ta sake nada Sanusi.
A cewar kotun daukaka kara, Mai shari’a Liman ya yi watsi da hurumin soke matakin da gwamnatin jihar Kano ta dauka bisa dokar majalisar masarautu ta 2024.
Ta kara da cewa, karar da wani basarake a jihar, Alhaji Aminu Babba Dan Agundi ya shigar, wanda alkalin babbar kotun ya dogara da ita wajen bayar da wannan umarni, ba ta da sahihanci.
Kotun daukaka karar ta ci gaba da cewa, tun da ba a bi ka’ida ba wajen shigar da ƙarar, hakan ne ya sanya ta rasa hurumin yin shari’ar.
A daya bangaren kuma, kotun daukaka karar ta bayar da umarnin sake zaman sauraron karar da Sarki Sanusi ya shigar na hana a fitar da shi daga Gidan Dabo.
Kotun daukaka karar ta bayyana cewa, shaidun da ke gabanta sun tabbatar da cewa ba a bai wa Sqrki Aminu Bayero damar jin ɓangaren sa ba daga babbar kotun jihar Kano wadda, hakan ya sanya kotun daukaka karar ta ce kotun ta jiha ta gudanar da shari’ar rashin gaskiya a kansa.
Mai shari’a Mustapha, wanda ya yanke hukuncin, ya ce an gudanar da shari’ar ne ba tare da sanarwar sauraro ga Sarki Aminu Bayero ba domin ya iya gabatar da nasa bangaren.