
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yayi kira ga ‘yan Najeriya kada su yanke tsammani, su ci gaba da mai fatan Alheri game da ayyukan da yake yi.
Ya bayyana hakane a wajan taron jam’iyyar APC na kasa da ya gudana a fadarsa.
Yace yana fatan ganin karin ‘yan Jam’iyyar Adawa suna shiga jami’iyyar ta APC.
Shugaban ya kuma gode da amincewar da aka bashi na shugabantar Najeriya.