Friday, December 5
Shadow

Ku daina sauraren karairayin kafafen sada zumunta ku goyi bayan shugaba Tinubu>>Wike ya gayawa Mutanen Abuja

Ministan babban birnin tarayya, Abuja, Nyesom Wike ya nemi mutanen Abuja da su daina sauraren karairayin da ake musu a kafafen sada zumunta.

Hakanan yace su daina sauraren ‘yan Adawa wadanda kansu ba a hade yake ba.

Ya bayyana hakane a wajan kaddamar da wani titi a Apo.

Inda yace a baya karairayi kawai ake musu amma a yanzu gashi ana fada da cikawa.

Wike ya jawo hankalinsu da su goyi bayan Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu dan shine ya musu aiki na zahiri.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Na taba yin asarar Gold na Naira Biliyan 1.5,Inji Hajiya Hafsa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *