
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya roki ‘yan Najeriya da su kara hakuri dashi inda yace su bashi lokaci.
Ya bayyana hakanne a yayin kaddamar da sashin farko na titin Calabar zuwa Legas ranar Asabar.
Yace yasan cewa har yanzu mutane suna cikin tsammanin samun sauki kuma yasan cewa ana cikin matsi amma yana kiran a kara hakuri, sauki yana zuwa.
Shugaba Tinubu yace za’a samu ci gaba sosai kuma farashin kaya zai sauka, suna kokarin kawar da rashawa da cin hanci a bangaren canjin kudi da bangaren sayar da man fetur.