Friday, December 5
Shadow

Ku shirya karin kudin wutar Lantarki dan ba zamu iya ci gaba da biyan Tallafin wutar labtarkin ba saboda ba kudi>>Gwamnatin Tarayya

Ministan wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, ya bayyana cewa, yanayin tattalin arziki yasa gwamnati ba zata iya ci gaba da biyawa ‘yan Najeriya tallafin wutar Lantarki ba.

Yace dan haka ‘yan Najeriyar su shirya fara biyan ainahin kudin wutar lantarkin da suke sha ba tare da tallafin gwamnati ba.

Yace akwai ‘yan Najeriya masu rauni da zasu ci gaba da samun tallafin gwamnati amma maganar gaskiya ba zasu iya ci gaba da biyan tallafin wutar ba nan gaba.

Yace a yanzu haka kamfanonin wutar lantarkin na bin Gwanatin bashin Naira Tiriliyan 4.

Ya bayyana hakane yayin ganawa da kamfanonin wutar lantarkin kan biyan bashin sa suke bin gwamnati.

Karanta Wannan  Ji yand Sojan Najeriya ya goge shafinsa na X bayan da aka zargeshi da Kiyyayya ga Musulunci

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *