
Ministan wutar Lantarki, Adebayo Adelabu ya baiwa ‘yan Najeriya hakuri kan rashin wutar da ake fama da ita a ‘yan kwanakinnan.
Ya bayyana hakane a ganawar da yayi da manema labarai a Abuja ranar Talata inda yace musamman a wannan lokacin zafin da ake ciki rashin wuta akwai damuwa.
Yace amma suna bayar da tabbacin nan ba da jimawa ba zasu gyara wutar.