
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party a zaben shekarar 2023 data gabata, Peter Obi ya bayyana cewa, kudaden da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ke karbowa Bashi, da Tallafawa ‘yan Najeriya yake yi da jari da ba haka ba.
Yace ana ta cewa babu kudi amma kuma gwamnati na ta kara ciwo bashi.
Ya ce wadanda aka baiwa su yi jari zasu samarwa wasu aikin yi ta hakane za’a samu saukin talaucin da ake fama dashi a kasarnan.