
Tsohon shugaban hukumar Fansho ta kasa, Abdulrashid Maina yayi zargin cewa kudaden da tsohon Ministan shari’a, Abubakar Malami ya sata sun fi Naira Biliyan 212 da EFCC ta gano yawa.
Yace yasan hakane saboda shi aikinsa ne gano kudaden sata.
Ya nemi a bashi aikin binciken Malami inda yace sai ya gano kudaden da ya sata duka.
Yace amma Biliyan 212 ba komai bane cikin kudaden da Malami ya sace.