Friday, December 5
Shadow

Kudin da ake zargin tsohon shugaban NNPCL da ma’aikatan sa da sacewa zasu iya fin wanda ake zargin tsohon shugaban babban bankin Najeriya, Emefiele da sacewa>>EFCC

Rahotanni sun bayyana cewa, hukumar yaki da rashawa da cin hanci, EFCC zata fara binciken tsohon shugaban kamfanin mai na kasa, NNPCL watau Mele Kolo Kyari.

Tare da kyari, akwai mutane 13 da suma za’a bincikesu wanda suka yi aiki tare dashi.

Wata majiya daga EFCC ta bayyana cewa, Tuni aka kama wasu daga cikin tsaffin ma’aikatan sannan ana kan bin sahun sauran dan suma a kamasu.

Majiyar tace sauran wadanda ake bincike tare da kyari sune:

Abubakar Yar’Adua, Mele Kyari, Isiaka Abdulrazak, Umar Ajiya, Dikko Ahmed, Ibrahim Onoja, Ademoye Jelili, da Mustapha Sugungun.

Sauran sune Kayode Adetokunbo, Efiok Akpan, Babatunde Bakare, Jimoh Olasunkanmi, Bello Kankaya da Desmond Inyama.

Karanta Wannan  A Zaman Da Muka Yi Da Ku Babu Wata Yarjejeniya Dake Da Alaka Da Cewa Ba Za A Kara Farashin Man Fetur Ba, Martanin Gwamnatin Tarayya Ga Kungiyar Kwadago

Ana zargin dai Kolo Kyari da ma’aikatansa sun sace kudaden da aka ware dan gyaran matatun man Najeriya da kuma yin karyar gyaran.

Tuni EFCC ta nemi a bata bayanai game da albashin tsaffin ma’aikatan da alawus dinsu dan ta fara bincike.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *