Tsohon gwamnan jihar Jigawa kuma jigo a jam’iyyar hamayya ta PDP, Sule Lamido ya zargi gwamnatin shugaban Najeriya, Bola Tinubu da ta Muhammadu Buhari da rashin gaya wa ‘yan ƙasa haƙiƙa gaskiya game da gwamnatocinsu.
Cikin wata hira da BBC, toshon gwamnan na jihar Jigawa ya ce gwamnatocin biyu sun fifita farfaganda a maimakon faɗa wa ‘yan ƙasa gaskiyar halin da ƙasar ke ciki.
Sule Lamido ya ce a shekarar da ta gabata gwamnatin Tinubu ta yi kasafin kuɗi na kusan Tiriliyan 30, kuma hukumomin tattara haraji na ƙasar sun ce sun tara naira tiriliyan 50, amma duk da haka gwamnatin Tinubu ta buƙaci cin bashin domin cike giɓi a kasafin kuɗin na shekarar da ta gabata.
”Ka yi kasafin kuɗinka da za ka kashe a duka shekarar a kan naira tiriliyan 30, sai kuma ka samu kuɗin shiga naira tiriliyan 50, kenan in za ka yi amfani da su kana da rarar naira tiriliyan 20, to bashin me kuma za ka ciyo”.?
Tsohon gwamnan na Jigawa ci gaba da cewa ”dama mulki ake yi na yaudara da rashin faɗar gaskiya, abin da yake akwai daban-dabna kuma da ake yi daban”.