Friday, December 5
Shadow

Kuma Dai: Kalli Bidiyon yanda Mamakon ruwan sama ya haifar da anbaliyya a Maiduguri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno sun tsere daga gidanjensu bayan wata mummunar ambaliya ta auka wa wasu sassan birnin sakamakon ruwan sama mai ƙarfin gaske.

Rahotonni daga birnin sun ce lamarin ya shafi unguwannin Damboa road da Moduganari Ngomari da Bulunkutu Abuja da sauransu.

An dai wayi gari da mamakon ruwan sama a faɗin birnin, lamarin da ya haifar da ambaliyar.

A shekarar da ta gabata ne aka samu wata mummunar ambaliya da ta raba fiye da mutum miliyan guda da muhallansu a birnin na Maiduguri.

Karanta Wannan  Dama can sai da na fada za'a sha wahala saboda gyaran da zanwa Najeriya amma duk da haka wasu na sukata>>Shugaba Tinubu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *