
Rahotanni sun bayyana cewa, farashin danyen man fetur da Najeriya ke fitarwa zuwa kasashen waje da ake kira da Brent crude oil ya sake faduwa.
Farashin a yanzu ya doso Dala $70 akan kowace ganga.
Hakan dai ya farune ranar Laraba inda aka alakanta dalilin da cewa Rasha ce dake shirin fara kara yawan man fetur din da take fitarwa zuwa kasuwar Duniya.
Hakanan Suma kungiyar Kasashe masu arzikin Man fetur, OPEC suna shirin kara yawan man fetur din da suke fitarwa wanda hakan zai iya kara karya farashin.
Kasancewar Najeriya a matsayin kasa wadda mafi yawan kudaden shigarta daga sayar da danyen man fetur suke zuwa yasa karayar farashin kewa kudaden shigar gwamnatin kasar barazana.