Monday, December 16
Shadow

Kumburin kafa ga mai ciki

Mai ciki zata yi fama da kumburin kafa, musamman idan cikin ya fara girma.

Hakan na faruwane saboda nauyin abinda ke cikinta.

Hakan nasa jini ya rage gudana a kafarki, Musamman idan ana yanayim zafi ko kuma kin dade a tsaye.

Bayan girman da abinda ke cikinki yake yi, a yayin da kike da ciki, yawan ruwan dake jikinki yana karuwa.

Hakan kuma nasa ciwon kafa.

Kafa da gwiwoyinki da tafin kafa da yatsu duk zasu iya kumbura.

Yayin da cikinki ke kara girma, kumburin shima zai rika karuwa a hankali.

Saidai wannan kumburi idan dai ba ya wuce lissafi ba, bashi da cutarwa ga Mahaifiya ko abinda ke cikinta.

Karanta Wannan  Maganin rage zafin nakuda

Alamomin dake nuna kumburin me ciki me cutarwane kuma yana bukatar kukawar likita

Idan lokaci guda kumburin ya karu a fuska, hannu da tafin kafa.

Idan ciwon kai me tsanani ya hadu da kumburi.

Ganin dishi-dishi ko kamar ana walkiya.

Tsananin zafi a saman cikinki.

Zafin kirji ko zuciya da yaki yin sauki bayan da kika sha magani.

Idan akwai rashin lafiya me tsanani.

Yin amai.

Abubuwan da zasu taimaka wajan rage kumburin kafa ga mai ciki

Ki daina dadewa a tsaye.

Ki rika saka takalmi ko safa wadanda ba zasu matse miki kafa ba, a kiyaye kada a rika saka takalmi me matse kafa.

Karanta Wannan  Alamomin cikin wata uku

Ki rika zama kina hutawa yanda ya kamata.

Ki rika yin tafiya me dan tsawo.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *