
Kundin bajinta na ‘Guinness World Records’ ya karrama matashiyar nan yar Najeriya Hilda Baci saboda girka dafa-dukar shinkafa mafi yawa a duniya.
A watan Satumban da ya gabata ne matashiyar ta yi wani gagarumin aikin girka dafa-dukar shinkafa mafi yawa cikin tukunya ɗaya a duniya.
Dafa-dukar shinkafa da ake yi wa laƙabi da ‘jollof’ abinci ne da ya shahara a ƙasashen Najeriya da Ghana da Senegal da Saliyo da Laberiya da ma wasu da dama.
Hilda mai shekara 28 a duniya ta yi shuhura ne a shekara ta 2023 bayan kafa tarihin kwashe lokaci mafi tsawo tana girki ita kaɗai, na tsawon sa’a 93 da minti 11